Shugaba Assad: Syria na goyan bayan shirin zaman lafiya

Shugaba Bashr Assad Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Bashr Assad

Syria ta kira taron gaggawa na kasashen larabawa, domin duba hanyoyin shawo kan rikicin da kasar ke fama da shi.

Kwana daya bayan da kungiyar kasashen larabawan ta dakatar da Syrian, saboda ta kasa aiwatar da wata yarjajeniyar kawo zaman lafiyar da aka cimmawa a farkon wannan watan, mahukuntan Syrian sun ce har yanzu suna goyon bayan shirin kawo zaman lafiyar.

Shugabannin Syria sun yi kira ga kungiyar kasashen Larabawan da ta tura wata tawagar ministoci zuwa kasar, domin ta kula da yadda ake aiwatar da yarjajeniyar kawo zaman lafiyar.

Dubun dubatar 'yan kasar Syriar sun yi zanga zanga, domin kokawa da dakatarwar da aka yiwa kasar daga cikin kungiyar Larabawan.

A birnin Hama, masu fafutuka sun ce dakarun tsaro sun harbe mutane hudu.

Yanzu haka kuma kasar Masar ta ce, tana adawa sosai da duk wani mataki da kasashen waje zasu dauka, na neman kaiwa kasar ta Syria hari, ko ma wacce irin hujja ke garesu.

A cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta ce, hadin kan kasar Syria, shine kan gaba a manufofin Masar.

Karin bayani