Kungiyar Amnesty ta soki gwamnatin sojin Masar

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International Hakkin mallakar hoto a
Image caption Kungiyar Amnnesty ta ce Majalisar Koli ta Mulkin sojin Kasar Masar na cigaba da gudanar da mulkin danniya irin na Shugaba Hosni Mubarak

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi kakkausan suka a kan majalisar sojin da ke mulki a Masar, tana mai cewa sojojin sun murkushe sauran fatan da 'yan rajin tabbatar da dimokuradiyya ke da shi, sun kuma kasa cika alkawuran da suka yi na kare hakkin bil Adama.

A wani rahoto da ta fitar, kungiyar ta Amnesty ta ce Majalisar Koli ta Mulkin sojin ta cigaba da gudanar da mulkin danniya irin na Shugaba Hosni Mubarak, wanda aka hambarar a watan Fabrairu.

Daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton, Muhammad Lutfy, ya shaidawa BBC muhimmin abin da ke damun kungiyar.

Muhammad Lutfy ya ce yadda ake gurfanar da farar-hula a gaban kotun soji, shi kanshi keta hakkin dan Adam ne na samun shari'a ta adalci.

Karin bayani