PDP ta cire gwamna Timiprye daga takara

Shugaba Jonathan na PDP Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Jonathan na PDP

Jam'iyar PDP mai mulki a Najeriya ta cire sunan gwamnan jihar Bayelsa, Timiprye Sylva, daga cikin jerin wadanda za su shiga takarar gwamnan jihar a zabe mai zuwa.

Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ne ya dauki wannan mataki, a cigaba da aikin tantance 'yan takarar da za su tsayawa jam'iyyar a zaben da za a yi badi.

Sai dai har yanzu uwar jam'iyar ta PDP ba ta fito fili ta bayyana dalilan daukar matakin ba.

Amma wasu masu sharhi na ganin cewa, hakan ba zai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Timiprye Silva da shugaba Goodluck Jonathan ba, wanda dan asalin jihar ne.

Jihar ta Bayelsa dai tana daga cikin jihohi biyar na Najeriya, inda ba a gudanar da zaben gwamna a bana ba, saboda sai a shekara mai zuwa ce wa'adin mulkinsu ke cika.

Karin bayani