Burtaniya zata gudanar da taron samun zaman lafiyar Somalia

Wani yaro dake fama da rashin abinci mai gina jiki a Somalia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Burtaniya tace Kasar Somalia na barazana kai tsaye ga muradun ta.

Fira Ministan kasar Burtaniya, David Cameron, ya ce kasarsa za ta karbi bakuncin wani babban taron kasa-da-kasa badi a kan yadda za a tabbatar da kwanciyar hanakali a Somaliya da kuma yakar fashi a teku.

Mista Cameron ya ce Somaliya na barazana kai tsaye ga muradun Burtaniya, yayin da Somaliyawa kuma ke fama da fatara da yunwa, wadanda ke kara ta'azzara sakamakon tashe-tashen hankula.

Mista Cameron ya kuma ce wajibi ne kasashen duniya su yi hobbasa don kalubalantar masu fashi a teku, su kuma tallafawa kasashen da ke yankin, sannan su tumbuke tushen rikice-rikice da tashe-tashen hankula a Somaliyar.

Karin bayani