Jawabin Shugaba Tantawi bai gamsar da masu zanga-zanga ba

Masu zanga-zanga a Kasar Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Kasar Masar sun nuna rashin gamsuwa dangane da jawabin Field Marshal Mohammed Tantawi

Ga alamu alkawarin hanzarta mai da mulki a hannun farar hula a Kasar Masar ya kasa gamsar da dubun-dubatar masu zanga-zangar da su ka yi dafifi a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Alkahira.

A jawabin da ya yi ta gidan talabijin, shugaban majalisar koli ta mulkin soji, Field Marshal Mohamed Hussein Tantawi, ya ce za a gudanar da zabukan majalisar dokoki a makon gobe kamar yadda aka tsara, sannan kuma za a gudanar da zaben Shugaban Kasa kafin watan Yulin badi.

Filed Marshal Tantawi ya ce lallai rundunar sojin, wacce majalisar koli ke wakilta, ba ta da sha'awar kankame mulki, don haka a shirye ta ke ta mika mulki nan take idan kuri'ar raba-gardama ta nuna bukatar haka.

Sai dai masu zanga-zangar sun ce wannan sassauci bai isa ba.

Karin bayani