Jama'atu Nasril Islam a Najeriya ta ja hankalin mahukunta

Tashe- Tashen hankula a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jama'atu Nasril Islam ta bayyana cewa dole gwamnati ta tashi tsaye wajen kawo karshen tashe- tashen hankulan dake aukuwa a arewacin kasar

A Najeriya kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta ce dole ne gwamnatin kasar ta tashi tsaye wajen hukunta duk wadanda aka tabbatar suna da hannu a tashe-tashen hankulan da ke aukuwa a arewacin kasar inda aka yi asarar rayuka da dama da kuma dukiya mai dimbin yawa.

Kungiyar ta kuma nuna rashin gamsuwa da irin kwamitocin da gwamnati ta ke kafawa domin bincikar rikice-rikicen da suka auku.

A wata takarda da ta rabawa manema labarai a Kaduna, Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta nuna damuwa a bisa rashin hukunta wadanda aka samu da laifuffuka a rikice-rikicen da ke aukuwa, inda take ganin ya kamata gwamnati ta sake lale.

Yankin arewacin Najeriya dai ya jima yana fama da tashe- tashen hankula masu nasaba da addini da kabilanci da kuma siyasa.

Rikicin baya- bayan nan dai shi ne wanda ya auku a garin Kafanchan dake jahar Kaduna

Karin bayani