Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar Kuwait

Masu zanga-zanga a Kasar Kuwait Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Kasar Kuwait na bukatar Firayim Ministan Kasar ya yi murabus

Dubban masu zanga-zanga ne suka mamaye majalisar dokokin Kasar Kuwait na wani dan lokaci.

Sun yi hakan ne kuwa bayan da 'yansanda su ka hana su yin maci zuwa gidan Firayim Ministan kasar, Sheikh Nasir Muhammad Al-Ahmad Al-Sabah, don neman ya yi murabus.

Wani wanda ya shaida faruwar al'amarin ya shaidawa BBC cewa masu gadi ba su hana masu zanga-zangar shiga majalisar ba.

Kasar Kuwait dai kankanuwar Kasa ce mai arzikin man fetur

Karin bayani