An kafa gwamnatin rikon-kwarya a Libya

Firayim Ministan Kasar Libya, Abdurrahim Al-Keib Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kafa sabuwar gwamnatin rikon-kwarya a Kasar Libya, wacce za ta shirya zabukan majalisar dokoki

Firayim Ministan Kasar Libya, Abdurrahim Al-Keib, ya ba da sanarwar kafa gwamnatin rikon-kwarya wacce za ta shirya zabukan majalisar dokoki kafin karshen watan Yunin badi.

Firayim Ministan Libyan mai rikon-kwarya ya ce an yi la'akari ne da cancanta wajen nadin mukaman na baya-bayan nan.

Ya kuma yi watsi da maganganun da ke cewa an kafa gwamnatin rikon-kwaryar ne tare da yin la'akari da irin gudummuwar da yanki ya bayar a lokacin boren da ya hambarar da gwamnatin Marigayi Kanal Gaddafi.

To sai dai wasu daga cikin wadanda aka nada fitattu ne a lokacin boren, wadanda suka hada da ministocin cikin gida da kuma na tsaro.

Mista Abdurrahim ya ce abin da gwamnatin rikon-kwaryar za ta baiwa fifiko shi ne ci gaba da kokarin kula da mutanen da suka samu raunuka da kuma kula da iyalan wadanda su ka yi yaki da dakarun Kanal Gaddafi.

A yanzu haka dai an kafa majalisar ministocin Kasar, amma wannan shine masomin tafiyar siyasar kasar.

Karin bayani