Zaben 'yan majalisar dokoki a Kasar Morocco

Zabe a Kasar Morocco Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jama'ar Kasar Morocco za su zabi 'yan majalisar dokoki

Yau ne jama'ar Kasar Morocco ke kada kuri'a a zaben majalisar dokoki, wanda kuma shi ne zabe na farko tun bayan da Sarki Muhammad ya kaddamar da sauye-sauyen tsarin mulki, sakamakon guguwar neman sauyin da ta kada a kasashen Larabawa.

Kundin tsarin mulkin dai ya ba da karin iko ga majalisar dokoki da kuma Firayim Minista, wanda zai fito daga jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar.

Sai dai kuma wasu 'yan rajin kawo sauyi a Kasar sun ce sauye-sauyen ba su wadatar ba

Wata mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya Zainab Ballami, ta fadawa BBC cewa ''Kundin tsarin mulkin, wanda daga shi ne zabukan suka samo tushe ba na dimokuradiyya ba ne, don haka ba wani sauyin da aka samu''.

Idan har mutane ba su fito sosai domin kada kuri'unsu ba, to hakan wata alama ce da ke nuni da cewar mafi rinjayen masu zaben ba su gamsu cewar sauye-sauyen da aka gudanar za su taimaka wajen gina tsari irin na dimokuradiyya mai inganci ba

Karin bayani