Sabbin tsare-tsare a shafin Bbchausa.com

hausa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabon shafin BBC Hausa

Daga ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba, shafin intanet na BBC Hausa zai kasance da sabon tsari dauke da sabbin abubuwa da zasu taimaka wajen samun bayanai da musayar su.

Labarun da muke dauke dasu da rahotanni na musamman zasu cigaba da kasancewa a shafin, amma kuma an canza tsarin yadda zai fi daukar ido da jan hankali da kuma saukin karanta wa.

Shafin kuma zai bada damar samun hoton bidiyo da kuma sauti na murya, wadansu kai tsaye wasu kuma na shirye-shiryenmu na baya.

Sabbin abubuwa:

Sabon tsarin shafi: Za a samu karin fili domin manyan labarai da bidiyo da kuma hotuna. Kuma manyan labarai za su nuna ko akwai labarai dake da nasaba da su.

Alamomi na zahiri: An inganta yanayin alamomi da bayanai akan kowanne labari don samun sauki akan shafin da za a samu labarin.

Shafukan Labarai: Idan ka latsa labari kai tsaye, za a iya ganin alamomi a gefen labarin da zai bada damar samun wasu labaran a shafin namu. Saka labarai masu nasaba da juna zai kasance a gefen labarin ko kuma a kasan shafin.

Bidiyo: Naurar kunna bidiyon za ta kasance babba kuma mai matukar inganci. Akwai sauki wajen samun wasu shafukan masu nasaba da bidiyo da na sauti a cikin shafin na bidiyo da na sauti. Abinda hakan ke nufi shi ne mai sha'awar bidiyo ko sauti ba sai ya leka wasu shafukanmu ba.

Labarai da dumi-dumi: Sabbin labaran da aka wallafa a shafin farko zasu dauki alamar dake nuna cewar ba a dade da wallafawa ba ko kuma akwai karin bayanai da aka saka cikin labarin.

Aika labari: Akwai matukar sauki da kuma sauri wajen aika labari ga abokai a shafukan zumunta kamarsu Facebook da Twitter.

Idan kuka fuskanci matsala a wannan sabon shafin, sai a shaida mana ta hanyar yin amfani da "Tuntube Mu" dake shafinmu.