Yadda aka karkasa miliyoyin dalolin Amurka a Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Najeriya ta karkasa dalar Amurka miliyan dari biyar a watan Oktoba

Wata mujallar tattalin arziki mai suna 'Economic Confidential' ta wallafa tsarin kason arzikin Najeriya a watan Oktoban da ya gabata, inda aka rabawa gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin kasar dalar Amurka miliyan dari biyar, wato kusan naira miliyan dubu dari bakwai da casa'in da biyar.

Tsarin kason arzikin kasar na watan Oktoban ya nuna cewa a rukunin jihohi masu arzikin man fetur, jihar Ribas ta karbi fiye da naira biliyan ashirin da biyu, su kuma jihohin Akwa Ibom da Delta sun karbi kusan naira biliyan ashirin da biyu, yayin da jihar Bayelsa kuma ta tashi da kusan naira biliyan goma sha hudu.

A rukunin jihohin da ba su da arzikin mai, amma su kan sami kaso mai tsoka kuma, jihar Legas ta sami fiye da naira biliyan goma sha shida, jihar Kano kuma ta sami kusan naira biliyan goma sha hudu.

Kana a rukunin jihohin da su kan sami kaso mafi kankanta irin su Nasarawa da Ebonyi da Ekiti, kowaccensu ta sami kasa da naira biliyan shida.

Karin bayani