An kwaso wasu 'yan Najeriya mazauna Libya zuwa gida

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kwaso wasu 'yan Najeriya mazauna Libya zuwa gida.

An kwaso wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Libya cikin daren jiya zuwa gida.

Kafin rikicin da ya kai ga kawar da marigayi Kanal Gaddafi dai, akwai 'yan Najeriya da dama da ke ci-rani a Kasar ta Libya.

Kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, Malam Yusha'u Abdulhameed, ya shaidawa BBC cewar jami'an ofishin jakadancin Najeriya dake Libyan ne suka tantance wadannan mutane kafin a kwaso su

Yawancin mutanen, a cewar kakakin hukumar, sun fito ne daga jihohin Edo da Lagos da kuma Imo a Kudancin Najeriyar

Hukumar ba da agajin gaggawar ta kuma bayyana cewar zata tabbatar mutanen sun koma gidajen su

A baya dai Najeiya ta taba tura jiragenta guda bakwai domin kwaso 'yan Kasar da rikici ya rutsa da su a Libyan

Karin bayani