Obama ya yi marhabin da shirin Abdallah Saleh na barin mulki

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obama ya yi marhabin da shirin Abdallah Saleh na barin mulki

Shugaba Obama ya yi marhabin da yarjejeniyar da Shugaba Ali Abdullah Saleh na Yemen ya rattabawa hannu wacce a karkashinta zai sauka daga mulki.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mark Toner, ya ce wannan muhimmin mataki ne

''Wannan ce hanyar matsawa gaba ga al'ummar Kasar Yemen, kuma muhimmin al'amari a matsawar shi ne aiwatar da wannan yarjejeniya'' in ji Mista Toner.

A karkashin yarjejeniyar dai wacce aka sanyawa hannu a Saudi Arabia, Shugaba Saleh ya amince ne ya mika mulki ga mataimakinsa, bayan ya kwashe watanni tara yana fuskantar zanga-zanga.

Karin bayani