Kasashen Larabawa za su gudanar da taro a kan kasar Syria

Taron Kungiyar Kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Kasashen larabawa za ta tattauna a kan rikicin kasar Syria yau a birnin Rabat na kasar Morocco

Kungiyar Kasashen Larabawa za ta gudanar da wani taro a yau don tattaunawa a kan rikicin kasar Syria.

Sai dai kuma tuni 'yan kasar Syrian su ka ce ba za su halarci taron na yau ba.

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa ne dai za su hadu a birnin Rabat na Morocco domin duba yiwuwar kara matsin lamba a kan gwamnatin kasar Syrian da nufin tilasta mata dakatar da tashe-tashen hankula.

A ranar Talata Fira Ministan kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kakkausan suka a kan Shugaba Assad inda ya ce yana son tunatar da shi cewar ba zai yiwu a gina makomar kasa da jinin wadanda aka zalunta ba.

Wasu masu sharhin al'amuran Kasashen Larabawa dai na ganin cewar da wuya a iya cimma wani abu a taron, ganin cewar kasar Syrian tace zata kauracewa taron.

Karin bayani