Masu zanga-zanga a Masar za su gudanar da sabon gangami

Masu zanga-zanga a Kasar Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Kasar Masar zasu gudanar da wani sabon gangami yau talata

Masu fafutuka a Masar sun yi kira ga al'ummar kasar su shiga wani gangami da za a gudanar yau Talata don kara matsin lamba a kan shugabannin mulkin sojin Kasar su mika mulki.

Dubban masu zanga-zanga ne dai suka kwana a dandalin Tahrir, to amma har yanzu yawan masu zanga-zangar bai kai wanda ya tilastawa tsohon shugaba Hosni Mubarak barin mulki a farkon shekara ba.

Jiya Litinin ne dai Majalisar ministocin kasar ta farar hula ta mika takardar yin murabus ga majalisar sojin.

Sai dai kuma har yanzu babu cikakken bayani a kan ko Majalisar sojin ta amince da murabus din.

Fiye da mutane ashirin ne suka rasa rayukansu a kwanaki ukun da aka kwashe ana tashe-tashen hankula a birnin.

Karin bayani