An yi Alla-wadai da yadda Syria ke keta hakkokin masu fafutuka

Shugaba Bashar Assad na Kasar Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dinkin duniya ta yi Alla-wadai game da yadda gwamnatin Syria ke keta hakkokin masu tabbatar da tsarin dumokiradiyya

Kwamitin kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a da gagarumin rinjaye ta yin Allah-wadai da yadda gwamnatin Syria ke keta hakkokin masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya.

Wannan kuri'a dai ta zo ne bayan Kasashen Rasha da China sun hau kujerar na-ki a kan yunkurin da aka yi na samun irin wannan kudiri a kwamitin sulhun majalisar.

Jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya, Bashar Ja'afari, ya zargi kasashen Yamma da haddasa boren da ake yi a kasar sa

Karin bayani