'Yan adawar Syria za su gana da Kungiyar larabawa

Zanga- Zanga a Kasar Syria Hakkin mallakar hoto a
Image caption Kungiyar kasashen larabawa zata gana da 'yan adawar kasar Syria nan gaba a birnin Alkahira

An gayyaci shugabannin 'yan adawa na Syria zuwa wani taro a shedikwatar Kungiyar Kasashen Larabawa da ke birnin Alkahira.

Kungiyar dai ta yi tayin aikewa da daruruwan masu sa ido don su duba halin da ake ciki a kasar ta Syria.

Wakilin BBC a Alkahira ya ce manufar taron ita ce taimakawa 'yan adawar su dinke barakar da ke tsakaninsu.

Tuni dai Amurka ta yi marhabin da karin matsin lambar da kasashen duniya ke yi kan Shugaba Bashar Al-Assad.

Wani mai magana da yawun fadar White House, Josh Earnest ya ce a zahiri Amurka ta yi marhabin da sanarwar da Kungiyar Kasashen Larabawan ta bayar cewa ta yanke shawarar dakatar da Syrian.

Kuma hakan a cewar sa na nufin gwamnatin Syria na kara zama saniyar-ware, sannan kuma matsin lamba a kanta na karuwa.

Karin bayani