An kammala yarjejeniyar raba mukamai a Tunisia

Shugaban jam'iyyar Ennahda, Rachid Ghannouchi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jam'iyyar Ennahda a Kasar Masar ta tsaida mukamin Firayim Minista bayan an kammala yarjejeniyar raba mukaman gwamnati

Manyan jam'iyyun kasar Tunisia sun cimma yarjejeniya a kan yadda za a raba mukaman gwamnati.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa mataimakin shugaban jam'iyyar masu matsakaicin ra'ayin addinin Islama wadda ta lashe kujeru mafi yawa a zaben watan jiya ta Ennahda, Hamadi Jebali, shi ne sabon Firayim Minista.

Shi kuwa shugaban jam'iyyar gurguzu ta Congress for the Republic, Moncef Marzouki, zai rike mukamin shugaban kasa ne, yayinda jagoran jam'iyyar Ettakatol, Mustafa Ben Jaafar, zai zama shugaban majalisar dokoki.

Majalisar dokokin ta wucin-gadi ce dai ke da alhakin tsarawa kasar sabon kundin tsarin mulki.

Karin bayani