Amurka ta kakabawa Iran karin takunkumi

Shugaba Ahmadinajad na Kasar Iran Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amurka ta bayyana bangaren hada-hadar kudaden Iran a matsayin wata cibiya da ke halalta kudin haram.

Amurka ta bada sanarwar kakabawa Kasar Iran wasu sabbin takunkumi da nufin durkusar da masana'antun man fetur din kasar.

Kasar Amurkar ta kuma yi gargadi ga kamfanonin da ke hulda da bangaren hada-hadar kudade na Kasar Iran, bangaren da ta ce cibiya ce ta halalta kudin haram.

Sakataren Baitulmalin Amurka Timothy Gethner, ya ce duk wata cibiyar hada-hadar kudade a ko ina a duniya na fuskantar hatsarin tallafawa miyagun ayyukan Iran, idan ta yi harka da babban bankin Iran ko ma sauran bankunan Kasar.

Tuni dai Kasashen Burtaniya da Canada suka bada sanarwar daukar irin wannan mataki.

Karin bayani