Shugaba Saleh na Kasar Yemen na shirin sauka daga mulki

Shugaba Abdallah saleh na Kasar Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A lokuta da dama Shugaba Saleh na Kasar Yemen ya sha yunkurin sanya hannu a kan yarjejeniyar barin mulki, sai kuma ya fasa.

Gidan talabijin din gwamnatin Yemen ya ce Shugaba Ali Abdallah Saleh ya isa Kasar Saudi Arabia, inda zai rattaba hannu a kan wata yarjejeniya wacce a karkashinta zai sauka daga kan mulki.

A jiya Talata wani wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman ya bayyana cewa, Shugaba Saleh ya amince ya mika mulki ga mataimakin sa, ya kuma karbi shirin kafa gwamnatin hadin-kan-kasa hannu bibbiyu.

Shugaban na Yemen dai ya sha fama da zanga-zangar nuna adawa da mulkinsa tun daga farkon wannan shekara, kuma a lokuta daban-daban a baya sai ya yi kamar zai sa hannu a yarjejeniyar ajjiye mulki sai ya fasa.

Karin bayani