An warware takaddamar Arik da British Airways

Filin jiragen saman Heathrow, London Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Filin jiragen saman Heathrow, London

Hukumar sufurin jiragen sama ta Birtaniya ta mayar wa kamfanin jiragen sama na Arik Airline na Najeriya damarsa ta sauka a filin jiragen sama na Heathrow dake London a kowace rana, daga Abuja, babban birnin Najeriya.

Haka nan kuma hukumomin Najeriya sun amince wa kamfanin jiragen sama na British Airways damar tashi daga filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas a kullum.

Wannan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da aka yi ne tsakanin mahukuntan Najeriya da takwarorinsu na Birtaniya kan wata takaddama tsakanin mahukunta sufurin jiragen sama a Najeriya da na Birtaniya bisa hana kamfanin Arik Airline sauka a filin jiragen sama na Heathrow a London.

Karin bayani