Turkiyya ta gargadi shugaba Assad

Rejep Tayyib Erdogan Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Rejep Tayyib Erdogan

Piraministan Turkiya, Recep Tayyib Erdogan ya gargadi shugaban Syria, Bashar al Assad cewa ba zaa iya gina Syria da jinin talakawan da aka danne ba.

Matakin Allah Waddai na baya-bayan nan da Mr Erdogan ya yi da gwamnatin Syria dai, ya zo yayinda kasashen duniya ke kara matsa lamba a kan hukumomin kasar ta fuskar Diflomasiyya da tattalin arziki, kan yadda suke murkushe masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar.

Ministocin kungiyar kasashen Larabawa za su yi wani taro a gobe; tuni kuma suka dakatar da Syriar daga cikin kungiyar saboda kin aiwatar da wani shirin zaman lafiya na kasashen Larabawan.

A halin da ake ciki kuma mahukuntan Syria sun bayyana sakin fursunoni fiye da dubu dake da hannu a zanga zanga.

Karin bayani