An tashi baram-baram a taron Abuja

shugaba Jonathan na Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption shugaba Jonathan na Nijeriya

A Najeriya, an tashi baram-baram a wata ganawar da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi da dukannin 'yan majalisar dokoki na tarayya.

A wajen taron dai Shugaba Jonathan ya nemi goyon bayan 'yan majalisar game da aniyar gwamnati ta janye tallafin da take bayarwa a bangaren man fetur.

Mafi yawan `yan majalisar, wadanda suka hada da na dattawa da kuma ta wakilai, sun ce ba su ga dalilin da zai sa gwamnati ta janye tallafin ba, kuma yin hakan zai jefa jama'ar kasar cikin wahala.

Bangaren gwamnatin kasar dai na zargin cewa wasu 'yan kasuwa kalilan ne ke cin gajiyar tallafin, saboda haka akwai bukatar a janye shi.

Karin bayani