Mario Monti ya kafa sabuwar gwamnatin Italiya

Pirayi Ministan riko na Italiya, Mario Monti ya ce ya kafa sabuwar gwamnati.

Da yake jawabi a fadar shugaban kasar a birnin Roma, Mr Monti ya gabatar da sunayen 'yan majalisar ministoci wadanda za a rantsar nan gaba a yau.

An shafe kwanaki biyu ana tattaunawa kafin a kafa sabuwar gwamnatin, bayanda Silvio Berlusconi yayi murabus a matsayin Pirayi Minista.

Italiya dai na fuskantar matsin lamba daga wajen kasuwanni hada-hadar kudi a duniya saboda dinbim bashin da ake binta.

Karin bayani