Shugaba Goodluck na ganawa da 'yan majalisa

A Najeriya, shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan na ganawa da `yan majalisar Dokokin kasar a fadarsa, da nufin shawo kansu game da aniyar gwamnatinsa ta janye tallafi daga bangaren mai.

Wannan dai shi ne karon farko da `yan majalisar za su yi tattaki zuwa fadar shugaban kasar don yin irin wannan tattaunawar.

Wasu na ganin zuwan 'yan majalisar dokokin kasar fadar shugaban kasa tamkar wani mika wuya ne ga bukatun gwamnatin. Sai dai kuma 'yan majalisar na cewa sam ba haka ba ne za su je ne kawai domin talakan Najeriya ya samu sauki ta batutuwan da taron zai mai da hankali.

Karin bayani