'Yan Nijer sun yi tsokaci akan farashin man fetur

Issoufou
Image caption Shugaba Issoufou na Nijer

A Jamhuriyar Nijar mutane na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da farashin man da Gwamnatin kasar ta ce za ta caza bayan ta soma tatar man da za a hako a kasar cikin watan gobe.

A jiya ne dai ma'aikatar ministan man fetur ta kasar ta bayyana sabon farashin .

Farashin da jama'a da yawa a Jahar Maradi dake iyaka da Najeriya ke ganin ba za su amince da shi ba.

A cewar wasu mazauna garin Maradi muddun gwamnatin Nijar ta ce za a yi aiki da wanann farashi, to sun gwammace sayen man daga Najeriya.

Karin bayani