Ana ci gaba da daukar matakai akan Syria

Taron kungiyar kasashen Larabawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron kungiyar kasashen Larabawa

Masu adawa da gwamnatin Syria sunce sojojin da suka sauya sheka sun kai hari akan wani sansanin tattara bayanan sirri na sojoji dake kusada da Damascus, harin da za a iya cewa shine wanda yafi muni kawo yanzu.

Rahotanni sun ce sojojin da suka sauya shekar wadanda ke kiran kansu "Free Syrian Army", sun harba rokoki akan ginin bayanan sirrin, wanda ake amfani da shi a matakan da ake dauka wajen murkushe 'yan adawa.

Wani dan kasar Syrian ya ce sakamakon cigaba da gallazawar da gwamnatin Assad ke yi, inda take kashe fararen hula wadanda basu da makamai, sojojin na bukatar 'yanci kuma sun sauya sheka daga dakarun sojojin gwamnati.

Wasu rahotannin da ba'a tabbatar da su ba sun ce sun ce an kashe sojojin gwamnati shida.

An kai harin a dai dai lokacin da ministocin hulda da kasashen waje na kungiyar kasashen larabawa ke taro a Morocco, inda ake saran zasu tabbatar da dakatar da Syria daga kungiyar.

A waje daya kuma Faransa ta bukaci jakadanta na Syria da ya koma gida.

Karin bayani