Burma zata jagoranci taron Asean

Taron  kasashen kungiyarAsean Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron kasashen kungiyarAsean

A karo na farko, Kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya sun amince da barin kasar Burma da ta jagoranci taron kungiyar kasashen yankin wato ASEAN wanda za'a yi a shekarar 2014.

Indonesia wadda ke jagorantar taron a bana ta ce Burma ta samu ci gaba ta fuskar demokradiyya.

Shugaba Obama dai ya ce wannan ci gaban ya sa Burma ta bude babin tattaunawa da sauye sauye, sai dai akwai bukatar inganta hakkokin Bil adama.

Inda yace har yanzu kiyaye hakkokin bil adama sun gagara, don haka za'a ci gaba da yin magana karara game da matakan da zasu dauka idan har gwamnatin Burma tana so ta kulla alaka mai kyau da Amurka.

Karin bayani