Dole ne Iran ta amsa tambayoyi- IAEA

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Hukumar makamashin Nukiliya ta duniya, Yukiya Amano.

Shugaban Hukumar makamashin Nukiliya ta duniya, Yukiya Amano ya ce dole ne Iran ta amsa tambayoyi game da yiwuwar shirinta na Nukiliya na daukar salon soji.

Da yake magana a wajen wani taro na wakilan hukumar zartas war hukumar makamashin Nukiliyar ta duniya, Mr Amano ya ce aikinsa ne ya ankarad da duniya game da ci gaba da damuwar da hukumarsa ke da shi cewar mai yiwuwa Iran na aiki a kan kera wani bam na nukiliya.

Iran dai ta musanta zargin.

Mr. Amano yace a bayyane yake akwai abin dubawa game da lamarin Iran, inda ya ce sama da shekaru ukun da suka gabata hukumar ta samu bayanan da ya kara mata haske game da shirin makashin nukiliyar Tehran.

Kuma ya ce yana son ya aike da wata tawaga mai karfi Iran don samun amsar wasu tambayoyi.

"Game da batun tattaunawa tun da fari na jaddada cewa ayi tattaunawa mai amfani da Iran kuma zan ci gaba da fadin hakan.

"Kuma na yi tayin aika wata babbar tawagar kwararru zuwa Iran don tattauna wasu muhimman batutuwa da ba'a tabo ba da suka hada da yiwuwar daukar matakan soji game da batun shirin nukiliyar Iran."

Kasar ta Iran dai ta ce rahoton Hukumar sa ido akan makamashi ta Majalisar Dinikin Duniya IAEA bai kunshi duka bangarorin da abin ya shafa ba.

Haka kuma ta zargi hukumar da zama 'yan amshin shatar Amurka.

Jami'an diplomasiyya a yanzu na kokarin cimma yarjejniya waraware batun, suna masu nuna damuwa game da batun shirin makamashin na Iran.

Sai dai basu kai ga gabatar da kokensu ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba wanda zai karawa kasar takunkumi.

Karin bayani