Tilas a tabbatar da doka da oda a Kuwait

Masu zanga zanga a Kuwait Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a Kuwait

Sarkin Kuwait ya ba jami'an tsaron kasar umarni na su dauki duk wani mataki da ya dace domin tabbatar da doka da oda a kasar.

Sheikh Sabah Al Ahmed Al Sabah ya ce ba za'a amince da duk wani abu da zai keta dokar kasar ba.

Wannan dai ya biyo bayan zanga zangar da dubban matasa suka yi a jiya laraba ne, wadda ita ce mafi girma da aka yi game da neman Praministan kasar da ya yi murabus.

Wani daga cikin masu zanga zangar ya bayyana cewa jama'a na san Praministan ya yi murabus, kuma a kafa demokradiyyar asali, inda za'a samu kundin tsarin mulki a masarautar kasar.