Gargadi kan gubar darma a Najeriya

Masu hako ma'adinai a Zamfara Hakkin mallakar hoto b
Image caption Masu hako ma'adinai a Zamfara

Majalisar Dinkin duniya ta yi kira ga mahukunta a Najeriya da su kara daukar matakan riga kafin kamuwa da cutuka masu nasaba da shakar gubar darma.

A cikin wannan makon ne, Majalisar ta ce ana samun wannan matsala a kauyuka akalla 43 na Najeriyar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO wadda ke taimakawa gwamnatin kasar wajen shawo kan matsalar ta yi kira ga hukumomin Najeriyar da su kara nuna azama wajen tunkarar lamarin ta hanyar kara mayar da karfi wajen bincikowa da kuma yiwa wadanda ke da cutukan magani.

Haka kuma ta bukaci da a tabbatar da an share gubar daga dukkanin wadannan yankunan dake jahar Zamfara a shiyar arewa maso yammacin kasar.

Daruruwan mutane ne dai suka rasa rayikansu a sanadiyyar kamuwar da cutukan dake da nasaba da shakar gubar ta darma a jihar Zamfara.

Karin bayani