Za a gudanar da bincike kan Shekarau game da cin hanci

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, ICPC ta ce za ta binciki tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, kan zargin saba ka'idar aiki a lokacin da yake jagorantar jihar.

Hukumar ta ce wata kungiya mai zaman kanta a jihar ta Kano ce dai ta kai karar tsohon gwamnan a wajen ta inda ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya ginawa kansa gida na kusan naira miliyan dari uku a lokacin da yake kan mulki, tana mai cewa hakan ya sabawa dokar aiki.

Mr Folu Olatumi, shi ne kakakin hukumar ICPC, ya ce hukumar na yin binciken ne a matakin farko.

Ya ce da zarar ta kammala binciken za ta san mataki na gaba da za ta dauka a kan tsohon gwamnan.

An mayar da martani

Sai dai bangaren tsohon gwamnan ya ce zuwa yanzu bai samu gayyata daga hukumar ta ICPC ba, amma a shirye yake ya amsa duk wata gayyata da hukumar za ta yi masa.

Kakakin tsohon gwamnan, Sule Ya'u Sule, ya shaida wa BBC cewa zargin wani yarfen siyasa ne da aka dade ana yiwa tsohon gwamnan.

Wannan dai shi ne karo na farko da wata hukuma ta ce za ta fara bincikar tsohon gwamnan kan zargin da ya shafi aikata ba daidai ba da kudaden al'ummar jihar Kano da ya shafe shekaru takwas yana mulka.

Dama dai 'yan adawa sun dade suna son ganin an gurfanar da Malam Shekarau a gaban kuliya bisa zargin cin hanci, su kuwa magoya bayan tsohon gwamnan cewa suke yi ba sa shakka domin ciki da gaskiya wuka ba ta fasa shi.