Jam'iyyar NLD ta tsayar da Aung San Suu Kyi

Aung San Suu Kyi
Image caption Aung San Suu Kyi

'Yar rajin kare demokradiyya a Burma Aung San Suu Kyi, tace za ta tsaya takara a zaben majalisar dokokin kasar, a wani gwajin dafin sunan da ta yi a shekaru ashirin.

Jam'iyyarta ta NLD ta sanar da cewa za ta yi rajista, bayan kauracewa zaben kasa baki daya a bara.

Wannan dai ya biyo bayan jerin sauye sayna da gwamnatin jeka nayinkan kasar ta yi ne da suka hada da sakin 'yan siyasar da ake tsare da su.

Tun da fari dai shugaba Obama, yace zai aika sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hilary Clinton Burma a watan gobe, shekaru hamsin kenan rabon da ayi hakan.

Karin bayani