Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi ki yaye da BBC Hausa: Bayanai a kan yaye

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kamar yadda muka alkawarta muku a makon da ya gabata, a wannan karon likita ta bayyana ma'anar yaye da kuma abubuwan da ya kamata uwa tayi ko ta sani game da yaye.

Mun baiwa yaye fassarori da dama da suka hada da yadda Hukumomin lafiya kamar na Birtaniya wato NHS da kuma sashen lafiya na BBC suka fassara inda suke cewa yaye wani mataki ne na fara janye yaro daga shan nono ta hanyar koya masa cin wasu nau'in abincin domin ya saba dasu kafin lokacin da zai daina shan nono kwata kwata.

Sai dai kuma yaye a al'adar Bahaushe na nufin janye yaron ne daga shan nono baki daya.

Akan yi amfani da matakai iri daban daban wajen daina baiwa yaro nono ta yadda zai saba kafin a janye baki daya. Wannan kuma ya danganta ne da al'ada ko kuma wani ra'ayi bisa radin kai da iyayen yaro kan yi amfani dasu wajen janye nonon baki daya.

Wasu ma kan dauke yaron zuwa wani gida domin ya manta da nonon baki daya, yayinda wasu kuma kan fara sabunta masa da abinci a lokaci guda kuma suna rage yawan nonon da yaro ke sha har ya zo ya saba ta yadda in an daina bashi ba zai damu ba, idan an yaye shi.

Shirin mu kenan na wannan makon. A yi sauraro lafiya.