Paparoma na fara ziyara a Afirka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Pope Benedict

A ranar Juma'a ne Paparoma Benedict ke fara wata ziyara a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin.

Yayin wannan ziyara dai ana sa ran Paparoman zai gatabar da wasu bayanai da za su fayyace yadda Cocin Roman Catholika za ta yi amfani da koyarwarta wajen shawo kan manyan matsalolin da ke fuskantar nahiyar Afrika.

Wannan ce dai ziyara ta biyu da Paparoma Benedict zai kai nahiyar Afrika.

Fadar Vatican ta ce, Paparoman zai iso ne da sakon zaman lafiya da kuma sasanta tsakanin al'umma.

Ana dai sa ran yayin wannan ziyara, Paparoman zai ziyarci makwancin Cardinal Berndin Gantin, wanda abokinsa ne, kuma dan kasar na farko da ya taba zama Bishop a fadar Vatican.