An hallaka mutane hudu a Bauchi

Hari a Najeriya
Image caption Hari a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a yankin Bogoro na jahar Bauchi, inda suka kashe mutane hudu, kana suka jikkata wasu karin biyar.

Bayanai sun ce da tsakiyar daren jiya ne maharan suka far ma kauyen Gargare dake yankin na Bogoro, dauke da makamai.

Hukumomin tsaro a jihar Bauchin sun ce suna ci gaba da bincike.

A baya bayan nan lamarin tsaro na cigaba da tabarbarewa a Najeriya, inda ake zargin hukumomi da yin sakaci - zargin da su ke musantawa.

Karin bayani