Paparoma na cigaba da ziyara a kasar Benin

Paparoma Benedict da shugaba Yayi Boni na Benin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Benedict da shugaba Yayi Boni na Benin

A ziyarar da yake a jamhuriyar Benin, Paparoma Benedict ya yi kira ga shugabannin Afirka da kada su sa mutanensu su kasa samun kyakyawan fata a rayuwa.

A lokacin da yake magana a birnin Cotonou, Paparoma ya ce bai kamata shugabannin su yi zagon kasa ga makomar jama'arsu ba, ta hanyar lalata rayuwarsu ta yanzu.

Paparoma Benedict ya kuma yi Allah wadai da yadda cin hanci da handama da kuma rashin gaskiya suka yi katutu a nahiyar Afirka.

Karin bayani