Hukumar kula da makamashi ta nuna damuwa game da Iran

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban hukumar I.A.E.A, Yukiya Amano

Hukumar kula da makamashi ta duniya, IAEA, ta amince da wani kuduri da ke nuna matukar damuwa kan shirin nukiliyar kasar Iran, amma bata dauki matakan ladabtarwa a kan kasar ba.

Kudurin ya biyo bayan wani rahoto da hukumar ta fitar a makon jiya, inda take gargadin cewa Iran na kan hanyar kera makamin nukiliya.

Matakin wata matsaya ce da aka cimma tsakanin kasashe shidan da ke jagorantar tattaunawa kan shirin nukiliya na Iran.

Kasashen sun hada da Amurka, da Burtaniya, da Faransa, da Jamus, da Rasha da kuma China.

Iran ta mayar da martani

Sai dai Iran ta ce matakin dodo-rido ne kawai, kamar yadda jakadan ta a hukumar ta IAEA, Ali Asghar ke cewa:

''An sha daukar matakai game da mu akan kera makamin nukiliya , har ma mun saba da su.Kai har kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ma ya dauki matakai akan mu, wadanda suka hada da kakaba takunkumi, amma hakan bai yi wani tasiri ba.

Hasalima, hakan sai kara wa Iran kwarin gwiwa ya ke yi game da yadda za ta samar da makamin nukiliyar da take yi, domin dalilan zaman lafiya.Kuma babu gudu, ba ja da baya''.

Karin bayani