Sabuwar tarzoma ta barke a Masar

Dandalin Tahrir Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dandalin Tahrir

Sabuwar tarzoma ta barke inda ake taho-mu-gama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a birnin Alkahira na kasar Masar.

Rahotanni sun ce a yanzu ana fafata wa tsakanin bangarorin biyu ne a gefen dandalin Tahrir, kusa da ma'aikatar cikin gida ta kasar.

Mutane goma sha uku ne suka mutu a cikin kwanaki biyun da aka kwashe ana tarzomar.

'Yan sandan sun yi ta dukan masu zanga-zangar da kulake, suna fesa musu barkonon tsohuwa, kai harma harbinsu suke yi da harsasan roba, a yunkurin da suke yi na tarwatsa su daga dandalin Tahrir.

Masu zanga-zangar dai sun mayar da martani inda suke jifan 'yan sandan da duwatsu.

Ana zargin gwamnatin soji

Masu zanga-zangar dai sun zargi gwamnatin sojin kasar da yunkurin ci gaba da kasance wa a kan mulki, kuma sun ce hakan ba za ta sabu ba

Gwamnatin dai ta ce za ta ci gaba da shirinta na gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, wanda za a gudanar a makon da ke tafe.

Ta yi kira ga jam'iyyun siyasar kasar da su taimaka wajen ganin an daina zanga-zangar da ake yi.

Karin bayani