Saif al-Islam zai amsa tambayoyi a Libiya

Saif al-Islam Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saif al-Islam Gaddafi

Masu gabatar da kara zasu fara yiwa Saif al-Islam Gaddafi tambayoyi a yau, a wani wuri na sirri inda ake tsare da shi, tun bayan da aka kama shi a ranar asabar.

Wani jami'i a ma'aikatar shari'a ta Libya ya shaidawa BBC cewa, babban mai gabatar da kara a kotun duniya mai hukunta manyan laifufuka, Luis Moreno Ocampo, zai gana da Saif al-Islam din idan ya je Libya.

Har yanzu dai ba a bayyana ranar da mista Ocampon zai je Libiyar ba.

Kotun duniyar na neman Saif al-Islam ne bisa zargin aikata laifufukan yaki.

Gwamnatin rikon kwaryar Libiya ta yi wa kotun alkawarin yi masa shari'a bisa adalci a cikin kasar Libiyar.

Karin bayani