Mutane sun hallaka a rikici a jahar Plateau

Jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

Rahotanni daga jihar Plateau sun ce, wani sabon tashin hankali ya barke a karamar hukumar Barikin Ladi, inda bayanai daga bangarorin da lamarin ya shafa ke nuna cewa, an kashe mutane akalla tara.

Lamarin dai ya faru ne daga jiya da dare zuwa wayewar garin yau, inda bangaren Fulani makiyaya da kuma 'yan Kabilar Berom ke zargin juna da kai masu hare-haren, zargin da dukansu ke musantawa.

Rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Plateau ta ce ta tura dakarunta zuwa yankin, domin tabbatar da doka da oda.

A 'yan shekarun daruruwan jama'a ne suka hallaka, aka kuma yi hasarar dimbin dukiya, a tashe tashen hankula masu nasaba da addini da kabilanci da kuma siyasa a jahar ta Plateau.

Karin bayani