Masu zanga-zanga a Masar za su gudanar da sabon gangami

Dandalin Tahrir Hakkin mallakar hoto other
Image caption Ko za a amince da murabus din ministoci?

Rahotanni daga Alkahira babban birnin kasar Masar na cewa majalisar ministocin kasar ta yi tayin yin murabus.

Hakan na faruwa ne, bayan kwanaki uku da aka kwashe ana tarzoma a kasar, inda wasu kungiyoyin masu fafutuka ke kira ga majalisar mulkin soja ta kasar da ta mika mulki ga wata gwamnati ta 'yan juyin juya-hali.

Hadin gwiwar kungiyoyi takwas ya soki lamirin majalisar mulkin sojan, ya zarge ta da kasancewa kan gaba wajen yin zagon kasa ga juyin juya-halin da aka yi.

Mutane akalla 33 ne aka kashe, aka raunata wasu kimanin dubu daya da dari takwas, a arangama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar, tun daga lokacin fara tarzomar ranar Asabar.

Majalisar koli ta mulkin sojan kasar ta Masar ta ce tana nazarin tayin murabus din ministocin.

Bayan shafe kwanaki uku ana arangama tsakanin masu zanga zanga da sojojin ne dai wasu masu fafutuka a kasar ta Masar suka nemi da gwamnatin sojin tayi murabus bayan da akalla mutane talatin da uku suka rasu yayinda daruruwa suka ji raunuka.

Hadakar wasu kungiyoyin hadin gwuiwa takwas ciki har da magoya bayan shahararren dan adawa Mohammed El Baradei sun fitar da sanarwa me kunshe da bukatun da suke nema daga gwamnatin.

Ayman Nour, dan takarar shugabancin kasar a can baya, ya bayyana bukatun ne bayan wani taron gaggawa na 'yan siyasa da, inda suke neman a kawo karshen tashin hankalin:

Yace bukata ta farko a sanarwar ita ce a gaggauta kawo karshen tashin hankalin da ake yi wa masu zanga zanga.

Sannan a shirya kafa sahihihin bincike na gaskiya da adalci game da duk wasu da ke da hannu a abin da ke faruwa a dandalin Tahrir da ma sauran dandalin dake kasar Masar.

Sauran bukatu sun hada da yin kira don yin zabe kamar yadda aka shiryi yi, tare da bincikar duk wani mai hannu a cin zarafin masu zanga zanga.

Karin bayani