Kotu ta wanke Alhaji Bello Lafiagi

Wasu buhunan miyagun kwayoyi da aka kama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu buhunan miyagun kwayoyi da aka kama

Yau ne wata kotun daukaka kara a Lagos ta wanke tsohon shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, Alhaji Bello Lafiagi daga zargin cin hanci da karbar rashawa.

A hukuncin da mai sharia'a Muhammed dan Juma ya yanke, ya nuna cewar hukuncin da tun farko wata babbar kotun ta yanke inda ta same shi da laifi, bai bi diddigin zargin ba kafin yanke hukuncin .

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da karbar rashawa ce dai ta shigar da karar, tana zargi tsohon shugaban hukumar da karbar kudi kimanin Euro dubu dari da 63 da 400 a hannun wani Mr. Ikenne Onuchi da ake zargi da fataucin hodar Ibilis.

Karin bayani