Libya ta ce ba za a mika Saif Gaddafi ba

Louis Moreno Ocampo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Louis Moreno Ocampo

Ministan shari'ar Libya ya ce ba za a mika Saiful Islam ga kotum hukunta manyan laifuka ba.

Mohammed Allagui ya ce za a yi wa Saiful Islam shari'a ne a Libya.

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifukka na kasa da kasa, Louis Moreno-Ocampo na wata ziyara a Libya don tattaunawa akan makomar Saiful Islam, dan marigayi Kanar Gaddafi, da aka kama a kwanakin baya.

Hukumomin Libya sun ce Luis Moreno Ocampo ya gana da Ministan Shari'ar kasar na rikon kwarya, da kuma babban maigabatar da kara na Libya, kuma yana so ne ya san irin matakan da mahukuntan

Libyar ke son dauka a kan Saiful Islam, da kuma Abdallah Al Sanusi, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar.

Karin bayani