An kashe fiye da mutane goma a jihar Filato a wani sabon tashin hankali

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto .
Image caption Taswirar Najeria

Rahotanni daga jihar Filato na cewa mutane kimanin goma sha biyar ne suka rasa rayuknsu a ranar Alhamis a Barkin Ladi, a tashin hankali mai nasaba da kabilanci da kuma addini da aka yi.

Wasu kuma karin mutanen da dama sun jikkata.

Haka kuma an yi kone-konen dukiya.

Tashin hankalin dai ya faro jiya da dare inda bangarorin biyu suka ba da labarin samun gawawwakin ‘yan’uwansu, suka kuma zargi junanasu da kisan, zargin da kowane ke musantawa.

Tun ranar Litinin da ta gabata ne dai zaman zullumi ya karu a yankin, sakamakon wani tashin hankalin da ya yi sandiyar mutuwar mutane goma.

Jihar ta Filato dai ta sha fama da irin wannan tashin hankali da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawan gasket da kuma dukiyoyi da dama.

Karin bayani