Human Rights Watch ta kushe korar Farida Waziri

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, sauke shugabar Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa daga kan mukaminta, ba shi ne zai magance matsalolin cin hanci da karbar rashawa a kasar ba.

Human Rights Watch ta ce, kamata yayi gwamnatin Najeriyar ta yi manyan sauye sauye ga kafofinta, in dai har tana son ta shawo kan lamarin cin hanci da rashawar a kasar.

A jiya ne dai shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya kori shugabar EFCC, Mrs Farida Waziri daga mukamin nata, ya kuma maye gurbinta da mataimakinta, Ibrahim Lamorde.