An kammala zaben shugaban kasa a Gambia

Yahya Jammeh, Shugaban Gambia
Image caption Yahya Jammeh, Shugaban Gambia

An kammala zaben shugaban kasar da aka gudanar yau a Gambia.

Shugaba Yahyah Jammeh, wanda ya kwaci mulki shekaru goma sha bakwai da suka gabata, shi ne ake kyautata zaton zai lashe zaben daga cikin 'yan takara ukku, inda zai yi kara wasu shekarun biyar a karagar mulki.

Shugaba Jammeh ya ce abin da ya yi wa kasar cikin shekaru goma sha bakwai da ya yi yana mulki sun zarce abin da aka yi wa kasar cikin shekaru dari hudu da Biritaniya ta kwashe tana yi wa kasar irin mulkin da bai dace ba.

Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS ko CEDEAO, ba ta tura masu sa ido a kan zaben ba, saboda a cewar ta, ba za a yi gaskiya da adalci ba.

Su ma dai kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi tir da yadda aka gudanar da yakin neman zaben, tana zargin ana musguna wa ‘yan adawa.

Sai dai Tarayyar Turai da kuma ta Afirka, sun tura nasu masu sa ido a zabe.