Ana ci gaba da zanga zanga a Masar

zanga zanga a masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zanga zanga a masar

Dubban masu zanga zanga ne suka taru dazu a dandalin Tahrir a Alkahira bayan sallar Juma'a suna bukatar jagoran majalisar mulkin sojan kasar ya yi murabus.

Sanarwar da aka yi cewa tsohon Pira ministan kasar Kamal Ganzouri ne zai jagoranci sabuwar gwamnati a kasar, da alama ba ta gamsar da da su ba.

Shi ma dan takarar shugabancin kasar wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel Mohammed El-baradei ya bi sahun masu zanga-zangar inda suke rera taken ba za mu tafi ba, shi ne zai tafi wato suna nufin Field Marshal Tantawi wanda ke jagorantar majlisar mulkin soji.

Tun da farko a masallacin Omar Makram wanda a baya ake amfani da shi a matsayin asibitin da ake jinyar wadanda suke samun rauni a zanga-zangar da ake yi a dandalin na Tahrir, limamin masallacin Mazhar Shaheen, ya jagoranci sallar Juma'a a wani masallaci dake wani bangare na dandalin.

An dai cika dandalin da tutocin kasar ta Masar masu ruwan ja da fari da kuma kore, dake da girma daban daban.

Karin bayani