Pirayim Ministan Masar yayi rokon da a ba shi dama

zanga zanga a masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption zanga zanga a masar

Mutumin da majalisar mulkin soji ta Masar ta nada domin zama Pirayim Ministan farar hula - Kamal El- Ganzoury, ya ce, zai kafa wata majalisar ministocin da za ta hada dukanin bangarorin siyasar kasar don yiwa jama'ar kasar aiki.

Yayinda Mr al -Ganzoury, ke wa kasar jawabi, dafifin jama'a sun sake mamaye dandalin Tahrir, suna neman a kawo karshen mulkin soji.

Wasu masu zanga zangar sun yi watsi da nadin Kamal al-Ganzoury, wanda ya taba yin Pirayim Minista a karkashin Shugaba Mubarak da aka hambarar.

A cikin jawabinsa, Mr Ganzoury, ya ce ba za a bayyana hadin sabuwar Gwamnatinsa ta cetar kasa kafin ranar litinin ba -- ranar da aka shata domin zaben majalisar dokoki na farko a Masar cikin shekaru.

Ana gudanar da wani gangamin mayar da martani na daruruwan mutane a wani dandalin a Alkahira domin goyon bayan soji da kuma Shugaba majalisar mulkin soji, Field Marshall Tantawi.

Masu zanga zangar dake karkada kwalaye da tutocin kasar, sun yi ta kururuwar sune ainihin yan kasar ta Masar.

Masu zanga zangar sun zargi masu zanga zangar dandalin Tahrir da wakiltar yan tsirarun Masar kawai.A halin da ake ciki kuma, Amurka ta bukaci da a mika mulki ga gwamnatin farar hula nan ba da jimawa ba.

Karin bayani