An kama mutane sama da dari a Filato

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumomi a jihar Filato ta Najeriya, sun ce sun kama mutane sama da dari da sittin dangane da rikicin karamar hukumar Barkin Ladi da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi.

Jami'an tsaro a jihar sunce ana ci gaba da yiwa mutanen tambayoyi.

A jiya ne dai aka yi wani tashin hankali, mai nasaba da kabilanci da addini a karamar hukumar ta Barkin Ladi.

Kawo yanzu hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane bakwai a rikicin an kuma kona gidaje masu yawa.

Mazauna garin dai na kokawa da halayyar jami'an tsaro da kama mutane hatta a cikin gidajensu, zargin da jami'an tsaron ke musantawa.

Hakazalika a bangare guda, jama'ar garin na kokawa da dokar nan ta hana fita ba dare ba rana da ke ci gaba da aiki har yanzu, suna cewa ta jefa su cikin mawuyancin hali.

Karin bayani